Zabura 150
Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; 
yabe shi a cikin sammai na ikonsa. 
 2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; 
yabe shi saboda mafificin girmansa. 
 3 Yabe shi da ƙarar kakaki, 
yabe shi da garaya da molo, 
 4 yabe shi da ganga kuna taka rawa, 
yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa, 
 5 yabe shi da kuge mai ƙara, 
yabe shi da kuge masu ƙara sosai. 
 6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. 
Yabi Ubangiji.