Zabura 3
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. 
 1 Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! 
Su nawa suke gāba da ni! 
 2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa, 
“Allah ba zai cece shi ba.” 
Sela
* Kalmar da ba a tabbatar da ma’anarta ba, mai bayyana sau da sau a cikin Zabura; mai yiwuwa kalma ce ta kiɗi.  3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; 
ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. 
 4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, 
ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. 
Sela
  5 Na kwanta na yi barci; 
na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. 
 6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma 
suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. 
 7 Ka tashi Ya Ubangiji! 
Ka cece ni, ya Allahna! 
Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; 
ka kakkarya haƙoran mugaye. 
 8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. 
Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. 
Sela
 
*Zabura 3:2 Kalmar da ba a tabbatar da ma’anarta ba, mai bayyana sau da sau a cikin Zabura; mai yiwuwa kalma ce ta kiɗi.