23
Faɗi 7 
 1 Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, 
ka lura sosai da abin da yake gabanka, 
 2 ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka 
in kai mai ci da yawa ne. 
 3 Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi 
gama wannan abinci ruɗu ne. 
Faɗi 8 
 4 Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; 
ka kasance da hikimar dainawa. 
 5 Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, 
gama tabbatacce sukan yi fikafikai 
sukan tashi sama kamar gaggafa. 
Faɗi 9 
 6 Kada ka ci abincin mai rowa, 
kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi; 
 7 gama shi wani irin mutum ne 
wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin.* Ko kuwa gama yadda yake tunani a cikinsa, haka yake; Ko kuwa gama yadda ya sa a bikin, haka yake 
Zai ce maka, “Ci ka sha,” 
amma zuciyarsa ba ta tare da kai. 
 8 Za ka yi amai ɗan abin da ka ci 
dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza. 
Faɗi 10 
 9 Kada ka yi magana da wawa, 
gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a. 
Faɗi 11 
 10 Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā 
ko ka ɗiba gonar marayu, 
 11 gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; 
zai kuwa yi magana dominsu. 
Faɗi 12 
 12 Ka mai da hankali ga umarni 
ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani. 
Faɗi 13 
 13 Kada ka bar yaro ba horo; 
in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba. 
 14 Ka hukunta shi da sanda 
ka ceci ransa daga mutuwa. 
Faɗi 14 
 15 Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, 
to, zuciyata za tă yi murna; 
 16 cikin cikina zai yi farin ciki 
in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai. 
Faɗi 15 
 17 Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, 
amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi. 
 18 Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, 
kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba. 
Faɗi 16 
 19 Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, 
ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai. 
 20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa 
ko masu haɗama kansu da abinci, 
 21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, 
gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki. 
Faɗi 17 
 22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, 
kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa. 
 23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; 
ka nemi hikima, horo da fahimi. 
 24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; 
duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa. 
 25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; 
bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki! 
Faɗi 18 
 26 Ɗana, ka ba ni zuciyarka 
bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina, 
 27 gama karuwa rami ne mai zurfi 
mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce. 
 28 Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira 
tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza. 
Faɗi 19 
 29 Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? 
Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? 
Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu? 
 30 Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, 
waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi. 
 31 Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, 
sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, 
sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro! 
 32 A ƙarshe yana sara kamar maciji 
da kuma dafi kamar gamsheƙa. 
 33 Idanunka za su riƙa gane-gane, 
zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa. 
 34 Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, 
kwance a sama itacen jirgin ruwa. 
 35 Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! 
Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! 
Yaushe zan farka 
don in ƙara shan wani?” 
*23:7 Ko kuwa gama yadda yake tunani a cikinsa, haka yake; Ko kuwa gama yadda ya sa a bikin, haka yake