19
Makoki domin sarakunan Isra’ila 
 1 “Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila  2 ka ce, 
“ ‘Mahaifiyarki zakanya ce 
cikin zakoki! 
Takan kwanta cikin ’yan zakoki 
ta kuma yi renon kwiyakwiyanta. 
 3 Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, 
ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi. 
Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta 
yakan kuma cinye mutane. 
 4 Al’ummai suka ji labarinsa, 
aka kuma kama shi cikin raminsu. 
Suka ja shi da ƙugiyoyi 
zuwa ƙasar Masar. 
 5 “ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba, 
abin da take fata gani ya tafi, 
sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta 
ta mai da shi zaki mai ƙarfi. 
 6 Ya yi ta yawo a cikin zakoki, 
gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi. 
Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta 
yakan kuma cinye mutane. 
 7 Ya rurrushe kagaransu 
ya kuma ragargaza biranensu. 
Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta 
sun tsorata da jin rurinsa. 
 8 Sai al’ummai suka tayar masa, 
waɗannan daga yankunan da suke kewaye. 
Suka yafa raga dominsa 
ya kuwa fāɗa cikin raminsu. 
 9 Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji 
suka kawo shi wurin sarkin Babilon. 
Suka sa shi cikin kurkuku, 
saboda haka ba a ƙara jin rurinsa 
a kan duwatsun Isra’ila ba. 
 10 “ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi 
da aka shuka kusa da ruwa; 
ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa 
saboda yalwan ruwa. 
 11 Rassanta suka yi ƙarfi, 
suka dace da sandar mai mulki. 
Ta yi tsayi 
zuwa sama 
ana ganin ta saboda tsayinta 
da kuma saboda yawan rassanta. 
 12 Amma aka tumɓuke ta cikin fushi 
aka jefar da ita a ƙasa. 
Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, 
aka kakkaɓe ’ya’yanta; 
rassanta masu ƙarfi suka bushe 
wuta kuma ta cinye su. 
 13 Yanzu an shuka ta a hamada, 
a busasshiyar ƙasa marar ruwa. 
 14 Wuta ta fito daga jikin rassanta 
ta cinye ’ya’yanta. 
Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta 
da ya dace da sandar mai mulki.’ 
Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”