Zabura 29
Zabura ta Dawuda. 
 1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, 
ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa. 
 2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; 
ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa. 
 3 Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; 
Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, 
Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye. 
 4 Muryar Ubangiji mai iko ce; 
muryar Ubangiji da girma take. 
 5 Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. 
Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu. 
 6 Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, 
Siriyon* Wato, Dutsen Hermon kuma kamar ɗan jakin jeji. 
 7 Muryar Ubangiji ta buga 
da walƙatar walƙiya. 
 8 Muryar Ubangiji ta girgiza hamada 
Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh. 
ya kakkaɓe itatuwan kurmi. 
Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!” 
 10  Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; 
Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada. 
 11  Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; 
Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.