47
Fāɗuwar Babilon 
 1 “Ki gangara, ki zauna a ƙura, 
Budurwa Diyar Babilon; 
ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba, 
Diyar Babiloniyawa.* Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a aya 5. 
Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi ’yar gata ba. 
 2 Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari; 
ki kware lulluɓinki. 
Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara, 
ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka. 
 3 Tsirararki zai bayyana 
za a kuma buɗe kunyarki. 
Zan ɗauki fansa; 
ba zan bar wani ba.” 
 4 Mai Fansarmu, Ubangiji Maɗaukaki shi ne sunansa, 
shi ne Mai Tsarkin nan na Isra’ila. 
 5 “Zauna shiru, tafi cikin duhu, 
Diyar Babiloniya; 
ba za a ƙara kira ke 
sarauniyar masarautai. 
 6 Na yi fushi da mutanena 
na ƙazantar da gādona; 
na ba su ga hannunki, 
ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba. 
Har ma da tsofaffi 
kin jibga musu kaya masu nauyi sosai. 
 7 Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, 
madawwamiyar sarauniya!’ 
Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa 
ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba. 
 8 “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, 
mai zama da rai kwance 
kina kuma ce wa kanki, 
‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. 
Ba zan taɓa zama gwauruwa 
ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’ 
 9 Duk waɗannan za su sha kanki 
cikin farat ɗaya, a rana guda, 
rashin ’ya’ya da gwauranci. 
Za su zo a kanki da cikakken minzani, 
duk da yawan masu dubanki 
da kuma dukan sihirinki. 
 10 Kin dogara a muguntarki 
kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ 
Hikimarki da saninki sun ɓad da ke 
sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’ 
 11 Bala’i zai fāɗo a kanki, 
kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba. 
Masifa za tă fāɗo a kanki 
da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba; 
lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba 
za tă auko miki nan da nan. 
 12 “Ki dai ci gaba, da sihirinki 
da kuma makarunki masu yawa, 
waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya. 
Mai yiwuwa ki yi nasara, 
mai yiwuwa ki jawo fargaba. 
 13 Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! 
Bari masananki na taurari su zo gaba, 
waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, 
bari su cece ki daga abin da zai faru da ke. 
 14 Tabbas suna kama da bunnu; 
wuta za tă cinye su ƙaf. 
Ba za su ma iya ceton kansu 
daga ikon wutar ba. 
Ba wutar da wani zai ji ɗumi; 
ba wutar da za a zauna kusa da ita. 
 15 Abin da za su iya yi miki ke nan kawai, 
waɗannan da kika yi ta fama da su 
kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya. 
Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa; 
babu ko ɗayan da zai cece ki.